Hausa Fashion Styles

4.5 (207)

Lifestyle | 37.8MB

Description

Wannnan application mai suna hausa fashion styles na dauke da kala-kala na kaya na sakawa na mata da maza da kuma huluna irin na zamani. yi downloding na wannan application domin taimaka maka wajen zaban diki iri daban daban da kake bukata na zamani.
Bayan hausa fashion styles idan akayi seaching adamsdut zakuma a iya samun application irin su
abinci hausawa (hausa food recipes)
magana jari ce
iliya dan mai karfi
ruwan bagaja da dai sauran su
Dan takaicecen tarihin hausawa.
Al'ummar Hausa dai, al'ummace dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Al'ummace mai dimbin yawa, sun bazu acikin kasashen Afirka da kasashen Larabawa kuma a al'adance masu matukar hazaka, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin wadanda harshen Hausa shine asalin yarensu. A tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno da kuma Fulani. A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa ke yinkurin kawar da mulkin Aringizo na Fulani, sai turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa karkashen mulkin Birtaniya,'yan mulkin mallaka sai suka marawa Fulani baya na cigaba da manufofin Aringizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin gamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a arewacin Nijeriya. Kodayake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da zuwan Addinin Musulunci da kuma karbansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam.
Ginshikokin al'adun Hausawa na da mutukar jarunta, kwarewa da sanayya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta.
Daura Kasace wacce a kasani mai dadewa da tarihi a kasar hausawa.
Sana'ar noma ita ce babbar sana'ar hausawa, sabo da ingancin noma; hausawa ke wa sana'ar noma kirari da cewa, "na duke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar", akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, sa'a da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in Hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana.
Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanayyar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cudeni-in cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa bane a nahiyar Afirka. Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacin Afirka da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin Hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan Turawa 'yan mulkin mallaka na birtaniya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka kirkiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

Show More Less

Information

Updated:

Version: 2.3

Requires: Android 4.1 or later

Rate

(207) Rate it

Reviews

Share by

You May Also Like